An hallaka ′yan jarida 80 a duniya a 2018 | Labarai | DW | 18.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka 'yan jarida 80 a duniya a 2018

Kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta kasa da kasa ta Reporters Sans Frontieres ta ce an hallaka 'yan jarida 80 a shekarar bana a fadin duniya da suka hada da maza 77 da mata uku.

Kungiyar ta bayyana wadannan alkaluma ne a rahotonta na shekara da ta wallafa, inda ta nuna damuwa dangane da yadda matsalar kisan 'yan jarida ko kuma cin zarafinsu ta kara ta'azzara idan aka kwatanta da shekar bara, inda aka kashe 'yan jarida 65 a kan aikinisu. 

Kungiyar ta ce 'yan jarida 700 ne aka hallaka a shekaru 10 na baya-bayan nan, kuma mafi yawancinsu an yi musu kisan da gangan ne kamar yadda ta kasance kan dan jaridar nan na kasar Saudiyya marigayi Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakdancin Saudiyya na birnin Santanbul din Turkiyya a ranar biyu ga watan Oktoban da ya gabata. Kasar Afghanistan ce a sahun kasashen da suka fi zama na ajalin 'yan jaridan a shekarar ta bana, inda aka halaka guda 15 a fagen aiki. 

Kazalika kungiyar ta Reportres Sans Frontieres ta ce adadin 'yan jaridan da aka tsare da su a gidajen kurkuku ya karu zuwa 348 sabanin 326 a bara, kuma rabinsu ana tsare da su a kasashe biyar da suka hada da Iran da Saudiyya da Masar da Turkiyya da kuma Chaina.