1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka Turawa biyar a kasar Habasha

January 18, 2012

Gwamnatin kasar Habasha ta yi karin haske bisa mutuwar turawa biya masu yawon bude ido a kusa da iyakar kasar da Eriteriya

https://p.dw.com/p/13lNo
meles mit flagge.jpg Ethiopian Prime Minister Meles Zenawi is seen during an interview with The Associated Press in the capital Addis Ababa Wednesday Nov. 1, 2006. Meles said Wednesday that Islamic militants in Somalia represent a threat to the Horn of Africa and the entire international community and that more must be done to contain them. (AP Photo/Les Neuhaus)
Meles Zenawi Firayim ministan kasar Habasha.Hoto: AP Photo

A kasar Habasha an hallaka mutane biyar yan yawon bude ido, wadanda yan asalin kashen Turai ne. Inda ake saran yan tawayen Habasha ne suka kai musu hari. Kakakin gwamnatin Habasha Bereket Simon ya fadawa manema labarai cewa, Turawan da aka hallaka sun hada da Jamusawa biyu, 'yan kasar Hungary kana da daya dan kasar Ostiriya, an kuma raunata Wani dan italiya da dan kasar Hungary. An kuma raunata wani dan kasar Italiya da daya dan kasar Hungary. Kawo yanzu ana ci gaba da yin garkuwa da Mutane hudu baki da dareban Turawan da kuma wani mai tsaron lafiyarsu. Farmakin dai an kai shine a lardin Afar dake kusa da kan iyakar Habasha da Eriteriya. Kasar Habasha ta dorawa makobciyar ta Eriteriya laifi, inda tace maharan suna samun mafaka ne a makobciyar ta, abinda kuma Eriteriya tace karya ce tsakwaron, wannan harkace da ta shafi cikin gidan kasar Habasha kawai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu