An hallaka ministan Falesdinu
December 10, 2014Talla
Shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas ya yi tir da kisan jami'in gwamnatinsa Ziad Abu Ain, da dakarun Isra'ila suka yi lokacin wata fafatawa a wannan Laraba.
Abbas ya ce za su dauki matakin gudanar da bincike sanain abin da ya faru. Shaidun gani da ido sun ce minista a gwamnatin Falesninawa Ziad Abu Ain dan shekaru 55 da haihuwa, ya rasa ransa lokacin da dakarun Isra'ila suka harba hayaki mai saka hawaye kan masu zanga-zanga a yankin Gaban Yamma da Kogin Jordan.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu