An halaka ma′aikatan jinya ′yan kasar Koriya a Najeriya | Labarai | DW | 10.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An halaka ma'aikatan jinya 'yan kasar Koriya a Najeriya

Arewacin Najeriya na neman zama wani gurin kisan baki'yan kasashen waje inda ake yawan kai musu hare hare ko kuma garkuya da su.

Wasu mahara da ba'a san ko su waye ba, sun hallaka wasu likitoci guda ukku 'yan asalin kasar Koreya masu aikin agaji a garin Potiskum mai nisan kilomita 100 daga Damaturu fadar gwamantin jihar Yobe jiya da dare ta hanyar musu yankan rago a gida.
Jami'an tsaro na jihar, sun tabbatar da aukuwar wannan lamari amma basu bada wani karin bayani ba inda suka ce suna kan gudanar da bincike. Ana dai yawaita kaiwa 'yan kasashen aziya hari a Najeriyar inda a watanin Octoba da Novamba,a kalla mutane hudu ne aka halaka 'yan asalin kasar China a Maiduguri.
Wanna kisan gillar dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake murnar samun zaman lafiya abinda kuma ake ganin zai iya maido da hannun agogo baya ga kokarin yin sulhu.

Mwallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal