1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Thailand: Hari ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro

Abdoulaye Mamane Amadou
November 6, 2019

Rundunar 'yan sandan a Thailand ta bayyana halaka jami'an tsaro 15 a wani harin da aka kai kan wani shingen bincike tare da raunata wasu da dama lardin Yala da ke kudancin kasar. 

https://p.dw.com/p/3SWvT
Thailand Anschlag in Yala
Hoto: Reuters/S. Boonthanom

Rahotanni sun ce an kai harin ne kan wani shingen jami'an tsaron a lardin Yala tare da wasu ababen fashewa, lamarin da kakakin rundunar tsaron yankin Kanal Pramote ya kira da aiyukan ta'addanci ne.Tun a shekarar 2004 ne dai lardunan da ke kudancin kasar Thailand da suka hada da Pattani da Narathiwat da Yala ke fama da hare-haren kungiyoyi sa kai masu gwagwarmaya da makamai, wadanda ake zargin cewa na tsananin kishin addinin Islama ne ke kai harin inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu bwakai.