An gwabza mummunar faɗa a gabacin Ukraine | Labarai | DW | 09.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gwabza mummunar faɗa a gabacin Ukraine

Ministan cikin gida na ƙasar Ukraine ya ce sojojinsu sun kashe dakarun `yan aware guda 20 a garin Marioupol da ke gabashin kasar.

Rahotannin daga Ukraine na cewar an gwabza faɗa a garin Marioupol da ke a yanki kudu maso gabashi ƙasar kan iyaka da Rasha, tsakanin dakarun gwamnatin da na 'yan aware masu goyon bayan Rasha. Ministan cikin gida na Ukraine Arsen Avakov ya ce: ''An kashe 'yan aware guda 20 magoya bayan Rasha, kana aka kama wasu guda huɗu sannan wasu 'yan sandarsu guda fuɗu sun jikata.''

Faɗan ya faru ne a lokacin da ake yin bukukuwan cikar shekaru 69 da kammala yaƙin duniya na biyu, kana kuma a lokacin da 'yan sanda na Ukraine suka yi ƙoƙarin sake ƙwato wata cibiyar jami'an tsaron da 'yan aware suka karɓe a yankni.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe