An gwabza fada tsakanin mayaka a Mali | Labarai | DW | 17.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gwabza fada tsakanin mayaka a Mali

Mutane da dama sun hallaka sakamakon kazamin fada da aka gwabza a yankin Anefis da ke a nisan kilo mita 120 Kudancin birnin Kidal.

Fadan dai ya faru ne tsakanin kungiyoyin biyu na mayakan Abzinawa, da suka hada da na kungiyar CMA ta "Coordination des mouvements de l'Azawad" da kuma ta hadin gwiwar mayakan Gatia masu goyon bayan gwamnatin kasar ta Mali. A cewar Fahad Ag Almahmoud, daya daga cikin jagororin mayakan hadin gwiwa na kungiyar Gatia masu biyayya ga hukumomin na Bamako, mayakan nasu sun hallaka mutane a kalla 15 cikin su har da jagororin mayakan na bangaran 'yan tawaye na CMA.

Sai dai daga nasu bangare 'yan tawayan basu bada wani adadi ba, amma kuma wata majiya daga bangare dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa na MINUSMA da ke arewacin kasar ta Mali, ta tabbatar da gwabza fadan. Inda ta ce sun samu labarin an yi fada tare da rasa rayuka, sai dai kuma babu wani bayani na adadin wadanda suka mutu daga bangarorin.