An gwabza faɗa tsakanin sojojin Mali da na MNLA
November 8, 2013Talla
Wasu majiyoyin soji sun ce an kashe dakarun ƙungiyar 'yan tawaye na Abzinawa su guda uku kana aka cafke wasu, yayin da ɗaya sojin gwamnati ya jikkata. Faɗan ya faru ne a sailin da wasu mutane ɗauke da makamai a yankin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar suka yi wa sojojin gwamnatin Mali kwanton ɓauna waɗanda ke yin sintiri.
Kuma faɗan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya kammala wata ziyarar aiki a ƙasar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh