An gurfanar da wanda da ya nemi harbe Trump a kotu | Labarai | DW | 21.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gurfanar da wanda da ya nemi harbe Trump a kotu

Wata kotu a birnin Las Vegas na kasar Amirka jiya Litinin ta tuhumi matashin nan dan Birtaniya wanda ya yi yunkurin kashe Donald Trump dan takarar jam'iyyar Republican da bindiga.

A ranar biyar ga watan Yuli mai kamawa ne za a gudanar da zaman shari'ar matashin mai shekaru 19 dan asalin Birtaniya wanda idan har kotun ta tabbatar da laifin da take zarginsa da aikata, tana iya yanke masa hukuncin zaman kaso na sama da shekaru goma da tarar kudi ta dalar Amirka dubu 250.

A ranar 18 ga wannan wata na Yuni ne dai a lokacin wani taron gangami da Donald Trump ya shirya a birnin las Vegas Michael Sandford dan shekaru 19 ya yi yinkurin kwace bindiga daga hannun wani jami'in tsaro amma lamarin ya ci tura. Kuma bayan an kama shi ya tabbatar da cewa yana da burin kashe Donald Trump din ne kawai.