1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da jana'izar Margaret Thatcher

April 17, 2013

Sama da mutane 2,300 daga sassan duniya ne suka halarci jana'izar tsohuwar priministar Britaniya Margaret Thatcher a birnin London.

https://p.dw.com/p/18HTC
Pallbearers carry the coffin of British former prime minister Margaret Thatcher into the hearse as it leaves the chapel of St Mary Undercroft at the Houses of Parliament during her ceremonial funeral in central London on April 17, 2013. The funeral of Margaret Thatcher took place on April 17, with Queen Elizabeth II leading mourners from around the world in bidding farewell to one of Britain's most influential and divisive prime ministers. AFP PHOTO / POOL / MIGUEL MEDINA (Photo credit should read MIGUEL MEDINA,MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images)
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

Dubban mutane ne suka yi jerin gwano a titunan birnin London domin yin bankwanar karshe wa tsohuwar priministan Britaniya mace ta farko, Margaret Thatcher, duk da ci gaban takaddama dangane da tarihin da ta bari. Titin Wesminster zuwa majami'ar St Paul Cathedral dai ya cika makil da mutane, a yayin da aka lullube akwatin gawarta da tutar Britaniya zuwa majami'ar domin yi mata adduo'i kafin jana'izar. Bishop Richard Chartres na london ya ja hankalin jama'a dangane da bukatar bawa Thatcher karramawa ta karshe, duk da baya da kura da mulkin da ta bari shekaru 23 da suka gabata ya bari.

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger da sarauniya Elizabeth ta Ingila da tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu na karshe a zamanin mulkin wariyar launin fata de Klerk, na daga cikin mutane 2,300 da suka halarci jana'izar tsohuwar priministan Britaniya Margaret Thatcher, wadda ta rasu a shekaru 87 a ranar litinin 8 ga watan Afrilu.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu