An gaza cimma matsaya kan rikicin Siriya
June 26, 2013Jakadan wanzar da zaman lafiya a Siriya na Majalisar Dinkin Duniya Lakhdar Brahimi ya ce babu tabbacin za a gudanar da taron tattauna batun rikicin Siriya a watan gobe kamar yadda aka shirya.
Wanna batu na Brahimi na zuwa ne a dai dai lokacin da aka gaza cimma matsaya tsakanin Amirka da Rasha, a kan shirin tattauna batun kawo karshen rikicin kasar Siriyan da yaki ci yaki cinyewa.
Bangarorin biyu sun samu banbancin ra'ayi kan lokacin da ya kamata a gudanar da babban taron na kasa da kasa kan Siriya da aka shirya gudanarwa a Geniva da kuma wadanda da zasu halarci taron.
Mukaddashin Ministan harkokin kasashen waje na Rasha Gennady Gatilov, ya ce har yanzu ba a cimma yarjejeniya game da ko Iran dake zaman babbar kawa ga Shuagaba Bashar al-Assad na Siriya za ta halarci taron ba, da kuma wandanda za su wakilci bangaren 'yan tawayen Siriyan yayin taron.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu