An gargadi al′ummar Masar da su guji tada rikici | Labarai | DW | 22.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gargadi al'ummar Masar da su guji tada rikici

Majalisar ministocin Masar ta yi kira ga jama'ar kasar da jam'iyyun siyasa da su tabbata sun guji tashin hankali yayin gangami ko zanga-zangar da su ke gudanarwa.

Majalisar ministocin ta yi wannan gargadi ne yayin taronta na farko da ta gudanar a wannan Lahadi (21.07.13) inda ta yi kira ga al'ummar kasar da su bada gudumawarsu ga sabon kwamitin da aka girka a kasar wanda zai yi garambawul ga kundin tsarin mulkin Masar din gabannin zaben 'yan majalisun dokokin kasar.

A daura da wannan, wani tashin hankali da aka samu a kasar ta Masar ya yi sanadiyyar kisan wasu sojoji biyu da dan sanda guda a yankin nan na Sinai yayin da daruruwan mata suka yi wani maci zuwa ma'aikatar tsaron kasar domin nuna fushinsu sakamakon kisan wasu mata uku da aka yi a wani gangami da magoya bayan hambararren shugaban Masar din Muhammad Mursi su ka yi a Mansura a ranar Juma'ar da ta gabata.

Zanga-zanga a Masar dai a dan tsakanin nan ta zama tamkar jamfa a Jos tun bayan da sojin kasar su ka hambarar da gwamnatin Mursi daga gadon mulki a farkon wannan watan.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh