An gano wasu kwarangwal da ka iya zama wani sabon jinsin dan Adam | Labarai | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano wasu kwarangwal da ka iya zama wani sabon jinsin dan Adam

'Yan kimiyya sun ce wasu kasusuwa da masu bincike suka gano a wani yanki da ke Afirka ta Kudu na da dangantaka da wani sabon jinsi na dan Adam.

Masana ilimin kimiyya sun ce sun gano wani sabon jinsi na dan Adam bayan wani bincike da suka gudanar kan wasu kasusuwa da kwarangwal da suka gano a wani kogo da ke kasar Afirka ta Kudu. Suka ce kasusuwan sun nuna wasu abubuwa na al'ajabi da ke kama da na dan Adam da ke da wasu alamu na zamanin jahiliyya, wanda wasu daga cikin 'yan kimiyyar suka bayyana da masu ba da tsoro. Shugaban masu bincike na jami'ar Witwatersrand da ke birnin Johannesburg na kasar ta Afirka ta Kudu, Farfesa Lee Berger ya ce kasusuwan za su haura shekaru miliyan 2.5. An ba wa wannan sabon jinsin sunan Homo Naledi.