An gano wani bangare na jirgin Air Asia | Labarai | DW | 07.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano wani bangare na jirgin Air Asia

Kasar Indunusiya ta bayyana cewa masu aikin ceto cikin tekun Java sun samu nasarar gano jelar jirgin Air Asia mai lamba 8501da ya fadi dauke da mutane 162 a watan jiya.

Shugaban aikin binciken na kasar Indunisiya Bambang Soelistyo ya bayyana haka a wannan Laraba, kwanaki 11 bayan fara wannan aiki. Ya ce sun sami nasarar gano wani sashi na jirgin wanda ke zama bangaren jelarsa. An kuma tsamo karin gawarwaki, inda zuwa wannan lokaci ake da gawarwakin da aka gano 40.

Masu binciken na fatar gano gangan jikin jirgin nan gaba kadan daga cikin tekun na Java. Ranar 28 ga watan jiya na Didamba ne jirgin saman dauke da mutane 162 ya yi hatsari lokacin da ya taso daga Surabaya na Indunusiya kan hanyarsa ta zuwa Singapoore, kuma ana kautata zatoncewa rashin kyaun yanayi ne ya janyo faduwar jirgin saman na Air Aisa.