An gano wanda ya kashe jagoran ′yan adawa na Tunisiya | Labarai | DW | 26.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano wanda ya kashe jagoran 'yan adawa na Tunisiya

Hukumomi sun ce wani ɗan Salafiya ne ya kashe Mohamed Brahimi wani dan adawar da aka harbe har lahira a tsakiyar wannan mako.

A cikin wani jawabin da ya yi ta gidan talbijan na ƙasar shugaba Moncef Marzouki, ya ce waɗanda suka aikata kisan, na neman zub' da darajar juyin juya halin da aka yi domin kawo tashin hankali.

Wani jagoran jam'iyyar adawa ta ƙasar mai sassaucin ra'ayi ta NIDAA Beji Caid Essebsi, ya ɗora alhakin kisan a kan gwamnatin masu kishin addini na jam'iyyar ENNAHADA. To amma a cikin wata sanarwa da ya bayyana ministan cikin gida na ƙasar Loftin Ben Jeddu, ya ce wani ɗan Salafiya wanda hukumomi ke nemansa ruwa jallo mai sunan Boubacar Hakim, wanda ya zo daga Libiya shi ne ya kashe Brahimi harma da Shokiri Belai wani jigon 'yan adawar shi ma da aka kashe a kwanan baya. Ministan ya kuma ce bindigar da aka kashe Shokiri Belai ɗin ita ce aka yi amfani da ita wajan hallaka Brahimi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu