An gano tarin makamai a Mali | Labarai | DW | 23.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano tarin makamai a Mali

Rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD a kasar Mali ce ta bankado wani rumbun daka boye tarin makamai a arewacin kasar mai fama da tashe-tashen hankula

An dai gano makaman ne a birnin Kidal, yankin da har yanzu ke fiskantar tashin hankali, tsakanin mayakan GATIA da ke samun goyon bayan gwamnati da kuma 'yan tawayen Buzaye masu neman kafa kasar Azawad. Inda ko da a makwan jiya aka hallaka mutane da yawa. Kakakin rundanar ta MDD da aka sani da MINUSMA, ya fadawa manema labarai cewa, masu sintiri da jiragen saman yaki ne suka gano tarin makaman, a wani yanki da ke kilo mita 50 daga birnin na Kidal. Ya kara da cewa makaman da aka gano, sun hada da tarin albarusai kala-kala da rokokin harba gurneti da wasu bama-bamai.