1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela: An kashe mutane ba bisa ka'ida ba

Abdul-raheem Hassan
July 4, 2019

Sabon rahoton majalisar dinkin duniya ya bankado yadda jami'an tsaro suka kashe mutane ciki har da 'yan adawa ta hanyar yi musu sharrin aikata laifukan ta'ammali da muggan kwayoyi da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/3LbGg
Venezuela Krise Polizei
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Llano

Binciken rahoton ya ce matakin jami'an tsaron na cikin dabarun gwamnati na murkushe 'yan adawa. Mutane 5,287 ne gwamnatin Venezuellan ta kashe a shekarar 2018 bisa zargin aikata laifuka, yayin da mutane 1,569 kuma aka kashe a watanni biyar na farkon shekarar 2019.

Rahoton ya gano cewa jami'an tsaron kasar sun yi wa mutane da dama sharrin aikata laifukan da ba su aikata ba kuma aka zartar da hukuncin kisa a kansu ba tare da gabatar da gamsassun hujjoji ba. Kasar Venezuella ta shiga radanin shugabanci tsakanin Shugaba Nicolas Maduro da jagoran adawa Juan Guaido. Mataklin da ya rarrabuwar kan manyan kasashen duniya kan wadan da suke marawa baya.