An gano na′urar bayanai na jirgin AirAsia | Labarai | DW | 12.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano na'urar bayanai na jirgin AirAsia

Sojojin ruwan Indonesiya da suka kware wajen iya linkaya a cikin teku sun bayyana cewa sun gano na'urar nadar bayanan jirgin AirAsia da ya yi hadari a watan da ya wuce.

Kimanin mutane 162 ne ke cikin wannan jirgi da aka gano na'urarsa kamar yadda shugaban shirin bincike da ayyukan ceto ya bayyana. Bambang Sulistyo ya ce da misalin karfe bakwai da minti goma sha daya a gogon kasar ne masu aikin ceto da bincike suka gano wannan na'ura da ake kira Black box a turance.

Sulistyo ya ce wannan na'ura na makale ne a fikafikin jirgi, an kuma gano inda wata na'urar da kan nadi magana take. Ita dai wannan na'ura za ta taimaka a aikin binciken da ake dan gano musabbabin hadarin.

Wannan jirgi mai lamba QZ8501 kafin hadarin, ya na kan hanyarsa ne daga garin Surabaya zuwa Singapore a ranar 28 ga watan Disamba inda ya bace wa na'urar da kan yi nazarin jiragen sama lokacin da suke tafiya a samaniya.