An gano gawarwaki 54 bayan rikicin kabilanci a Guinea | Labarai | DW | 17.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gano gawarwaki 54 bayan rikicin kabilanci a Guinea

Rikicin da al'ummomin kauyukan Guerze da Konianke suka shafe kwanaki biyu suna yi da juna yayi sanadiyar mutuwar mutane da ba a tantance yawansu ba.

Wani likita a Conakry babban birnin kasar Guinea ya ce an gano gawarwakin mutane 54 wadanda ko dai an konesu kurmus har lahira ko kuma daddatsa su aka yi da adduna lokacin rikicin kabilanci da ya auku a kudu maso gabacin wannan kasa dake yammacin Afirka. Likitan ya ce za su koma kauyukan Guerze da Konianke wadanda suka shafe sama da awowi 48 suna bata-kashi da juna a N'Zerekore babban birnin lardin kudancin kasar. Likitan ya kara da cewa har yanzu akwai gawarwakin da ba a tantance su ba saboda sare kawunansu da aka yi. Da farko dai kakakin gwamnatin kasar ta Guinea Albert Camara ya ce rigingimun da aka yi fama da su a yankin kudu maso gabashin kasar sun yi sanadiyar mutuwar mutane 17 sannan 80 sun samu raunuka. Kakakin ya kara da cewa yanzu haka an girke sojoji a birnin N'Zerekore, don mayar da bin doka da oda a birnin dake zama na biyu mafi girma a kasar ta Guinea. Sai dai har yanzu ana cikin zaman dar-dar a yankin. A cikin watan Satumba ake shirin gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a Guinea mai fama da tashe tashen hankula.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar