1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wanda ake zargi a mutuwar 'yar Britaniya

Ramatu Garba Baba
December 9, 2018

'Yan sanda a kasar New Zealand sun gano gawar da suke kyauta zaton na Grace Millane 'yar Britaniya da ta bata tun daya ga wannan watan na Disamba a wani yanki da ke Auckland na kasar.

https://p.dw.com/p/39ky0
Neuseeland Auckland - David Millane auf der Suche nach seiner vermissten Tochter Grace Millane
Hoto: picture-alliance/AP Photo/NZ Herald/D. Sherring

An dai fadada bincike da kuma neman matashiyar a duk fadin birnin na Auckland. A jiya Asabar 'yan sanda suka kama wani mutum dan shekaru ashirin da shida da aka yi wa gani na karshe da ita. An kuma shirya gurfanar da shi a gaban kuliya a gobe Litinin bisa zargin hannu a mutuwarta.

Tuni mahaifin matashiyar ya isa kasar inda ya mika sako ga duk wanda ke rike da ita ko ya san inda ta ke da ya tausaya ya sanar da hukuma. An dai kwashi kwanaki ana neman matan kafin a gano gawar a wannan Lahadin.  Grace Millane mai shekaru ashirin da biyu da haihuwa, ta na yawon zagaye duniya ne bayan da ta kamalla karatunta na jami'a kafin ta gamu da ajalinta.