An fara zaben ′yan majalisa a Birtaniya | Labarai | DW | 08.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara zaben 'yan majalisa a Birtaniya

A yakin neman zaben dai jam'iyyar Labour karkashin jagoranci na Jeremy Corbyn ta yi amfani da hare-hare da aka kai a Manchester Arena da Gadar London wajen caccakar gwamnatin Firaminista May.

Al'umma a Birtaniya sun fita tashoshin kada kuri'a a wannan rana ta Alhamis domin zaben 'yan majalisa a zaben da Firaminista Theresa May ta gaggauta matso da shi, sabanin yadda aka tsara tun da fari.

Batutuwa da suka hadar da tsaron cikin gida dai na zama a kan gaba a lokacin yakin neman zaben da jam'iyyar Labour karkashin jagoranci na Jeremy Corbyn ta yi amfani da hare-hare da aka kai a Manchester Arena da Gadar London wajen caccakar gwamnatin Firaminista May. Masharhanta dai na kallon masu ra'ayin mazan jiya a matsayin wadanda za su iya kwashe kujerun 'yan majalisar ko kashi biyu bisa uku a zaben da masu kada kuri'a sama da miliyan 30 za su fita.