1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Serena William na neman lashe kofi

Mouhamadou Awal Balarabe
August 28, 2018

A wannan Litinin din ce a birnin New York na Amirka aka fara daukar nauyin gasar Open ta Tennis, inda ake sa ran shaharuran 'yan wasa za su fafata tsakaninsu a rukunonin maza da na mata.

https://p.dw.com/p/33tAP
Wimbledon Serena Williams
Hoto: Getty Images/J. Tallis

'Yar Amirka serena williams wacce ta taba lashe manyan gasanni 23 cikin tarihinta za ta kara ne Magda Linette 'san kasar Poland a rukunin mata tun a ranar farko, Yayin da Venus Williams za ta yi wasa da Svetlana Kuznetsova ta Rasha.

Ita dai Serena Williams wacce ta haihu shekarar da ta gabata, ta na neman lashe kofin Open na New York don kamo kafar Margret Court wacce ta ke da nasara 24.

Yayin da a rukunin maza kuwa  Rafael Nadal dan kasar Spain mai nasara (17), zai yi wasan farko da David Ferre wanda ya taba samun matsayi na uku na duniya kafin reshen ta juye da shi har ya koma matsayi na 148.