An fara shirye-shiryen zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 08.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara shirye-shiryen zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

An fitar da sunan tsohon shugaban jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize daga cikin 'yan takara a zaben shugaban kasa da ke tafe.

An fitar da sunan tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize daga cikin 'yan takara a zaben shugaban kasa da aka shirya ranar 27 ga wannan wata na Disamba. A cikin watan Agusta Bozize ya bayyana shirin komawa domin ya yi takara.

Wani mai magana da yawun jam'iyyar tsohon shugaban ya ce kotun tsarin mulki ta fitar da wasu matakai masu sarkakiya domin hana tsohon shugaban tsayawa zaben.

Shi dai Bozize cikin shekara ta 2013 'yan tawayen kungiyar Seleka galibi Musulmai suka kawo karshen gwamnatinsa, abin da ya jefa kasar cikin rikicin tsakanin kungyoyi masu dauke da makamai na Seleka Musulmai da kuma anti-Baleka Kiristoci, lamarin da ya tagaiyara kasar. Tun farko an tsara zaben kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a watan Agusta, kafin daga bisani aka mayar zuwa wannan wata na Disamba.

Akwai 'yan takara 30 da aka amince da su yayin da 15 aka yi watsi da takardunsu da suka hada da tsohon Shugaban Francois Bozize. Za kuma a yi takara na kujerun majalisar dokoki 141. Akwai masu zabe kimanin milyan biyu, idan babu dan takara da ya samu kuri'un da ake bukata a zaben shugaban kasar, za a yi zagaye na biyu ranar 16 ga watan gobe na Janairu.