An fara shirye-shiryen kwance wa dakarun gwamnatin Côte d’Ivoire ɗamararsu. | Labarai | DW | 18.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara shirye-shiryen kwance wa dakarun gwamnatin Côte d’Ivoire ɗamararsu.

A ƙasar Côte d’Ivoire, an fara shirye-shiryen kwance wa dakarun da ke nuna biyayya ga gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo ɗamara, gabannin zaɓen ƙasar da za a gudanar a cikin watan Oktoba, da nufin haɗe kan ƙasar baki ɗaya. Kwamandan cibiyar tsara manufofin rundunar gwamnatin, Laftanan Kanar Rene Sacko ne ya bayyana haka yau a birnin Abidjan. A cikin wata fira da ya yi da kamfanin dillancin labaran AFP, kwamandan ya bayyana cewa, za a ci gaba da shirin ne har zuwa ran 28 ga wannan watan, amma bai ba da adadin sojojin da shirin zai shafa ba, wai saboda matakan tsaro.

A halin da ake ciki dai, ƙungiyoyin ’yan tawaye da ke riƙe da yankunan arewacin ƙasar, sun ce ba su ma fara tara dakarunsu a gu ɗaya ba tukuna, balantana ma a yi batun kwance musu ɗamara. Kakakin ƙungiyar, Sdiki Konate, ya faɗa wa maneman labaran kamfanin AFP cewa, ba za su fara kwance wa mayaƙansu ɗamara ba, sai shugabannin rundunar sojin ɓangarorin biyu masu hamayya da juna, sun cim ma yarjejeniya kan yin hakan.