1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara nuna damuwa kan siysan Italiya

December 11, 2012

Firaministan kasar Italiya Mario Monti ya kare matakin gwamnatinsa na daukan matakan tsuke bakin aljihu

https://p.dw.com/p/16zrk
Hoto: Reuters

Firaministan kasar Italiya Mario Monti ya kare matakin gwamnatinsa na daukan matakan tsuke bakin aljihu, wanda ya ce shi ne kawai zai sake dawo da martabar tattalin arzikin kasra nan gaba.

Sannan ya gargadi masu zabe kan su kula da 'yan siyasa masu romon baka na cewa su na da maganin sha yanzu magani yanzu, wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

Monti ya ce zai ajiye aikin da zaran majalisar dokokin kasar ta Italiya ta amince da kasafin kudin da ya gabatar mata, kuma ana saran gudanar da zaben a farkon shekara mai zuwa.

Tuni tsohon Firaministan kasra ta Italiya Silvio Berlusconi ya bayyana aniyar sake takarar mukamun yayin zaben da ke tafe.

A wani labarin Ministan Harkokin Wajen Jamus Guido Westerwelle, ya yi gargadin cewa Tarayyar Turai za ta shiga cikin kasada muddun aka tsayar da sauye sauyen tada komadan tattalin arzikin kasar Italiya.

Wannan sakamakon faduwar hanun jari Italiya da na Turai, sakamakon shirin tsohon firiminista Silvio Berlusconi na sake dawowa fagen siyasar kasar ta Italiya.

Ministan harkokin wajen na Jamus ya shaida haka wa manema labarai a Berlin babban birnin Jamus.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi