An fara korafin magudin zabe a Kenya | Labarai | DW | 06.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara korafin magudin zabe a Kenya

A yayin da ake zaman dakon sakamakon zabubbukan da aka gudanar, hadin gwiwar jam'iyun da suka mara wa Uhuru Kenyatta baya,sun fara nuna damuwar aringinzon kuri'u.

Masu aiko da rahotani daga kasar Kenya, sun bayyana cewar yanzu haka ana ci-gaba da zaman jiran sakamakon zabubbukan da aka gudanar a ranar Litanin da ta gabata.
To sai dai tuni hadin gwiwar jam'iyun da suka mara wa dan takara Uhuru Kenyatta baya, wanda kuma sakamakon dake fitowa daga wasu rumfunan zaben ke bayyanawa a matsayin mutumen da ke kan gaba da yawan kuri'u, sun fara nuna damuwarsu bisa ga abun da suka kira shirye shiryen ariginzon kuri'u.
Wata mai magana da yawun hadin gwiwar jam'iyyar Charity Ngilu, ta ce akwai bukatar aza ayar tambaya a dan gane da yadda hukumar zabe ta kasa ke tsare tsarenta a yanzu, inda suka samu labarin cewa hatta kuri'un da aka kada ba bisa ka'ida ba za a yi amfani da su, abun da kuma zai iya kawo wa jam'iyar ta Kenyatta cikas gurin lashe zaben a zagayen farko.
Ayar doka mai lamba 138 ta kundin tsarin milkin kasar dai, ta ce duk dan takarar da ya samu rabin yawan kuri'un da aka kada ,to babu shakka zai lashe zaben ba tare da an je zagaye na biyu ba.
Yanzu haka hankalin kasashen duniya ya karkata a wannan kasa wacce ta fuskanci tashe tashen hankula a yayin zaben da aka gudanar a shekara ta 2007.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mouhamadou Awal Balarabé