An fara kidayar kuri′u a zaben Indonesiya | Labarai | DW | 09.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kidayar kuri'u a zaben Indonesiya

'Yan takara biyu a zaben shugaban kasar Indonesiya sun bayyana kawunansu a matsayin wadanda suka lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Rahotanni daga kasar Indonesiya na nuni da cewa gwamnan Jakarta Joko Widodo ne ja gaba a kuri'un da aka fara kidayawa da kimanin kaso 53 cikin 100 yayin da shahararren dan kasuwa kuma tsohon janar din soja Prabowo Subianto ke biye masa da kimanin kaso 48 na yawan kuri'un da aka kidaya. Kuri'un dai an kidaya su ne a matsayin gwaji inda aka kidaya kaso daya na baki dayan kuri'un da aka kada. A ranar 22 ga wannan wata na Yuli da muke ciki ne dai ake sa ran samun sakamakon zaben shugaban kasar ta Indonasiya a hukumance, sai dai tuni gwamnann na Jakarta Joko Widodo ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da a hannu guda shima Prabowo Subianto ya bayyana cewa shi ne ya lashe zaben.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu