An fara kada kuri′a a Sri Lanka | Labarai | DW | 08.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kada kuri'a a Sri Lanka

Rumfunan zabe sun bude a Sri Lanka, inda ake gudanar da zabe mai cike da rudani don adawa da ta-zarce

Tun safiyar yau ne dai aka fara kada kuri'a na saben shugaban kasa a kasar ta Sri Lanka, inda shugaba mai ci Mahinda Rajapaksa, ke neman yin ta-zarci karo na uku, bayan da majalisar dokoki ta goge ayar doka da ta kayyade wa'adi sau biyu ga shugaban kasa. 'Yana dai karawa da tsahon ministan kiwon lafiya a gwamnatinsa, wanda ya bar jam'iyya mai mulki a watannin biyu da suka gabata. Tsohon ministan kiwon lafiya yace, muddin ya ci zabe zai rage karfin da aka baiwa shugaban kasa, kana zai yaki cin hanci wanda ya addabi gwamnati mai ci.