An fara gudanar da zaɓe a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 07.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara gudanar da zaɓe a Afirka ta Kudu

Ana sa ran Jacob Zuma na jami'yyar ANC ta marigayi Nelson Mandela zai sake samun nasar a zaɓen duk kuwa da zargin cin hanci da gazawa da 'yan adawa ke yi wa gwamnatinsa.

Al'ummomin ƙasar Afirka ta Kudu sun fara ƙada ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisun dokiki wanda a kansa za su zaɓi wakilai 400, waɗanda su kuma daga baya zaɓaɓin 'yan majalisun za su zaɓi shugaban ƙasa a ranar 21 ga wannan wata.

Shugaba Jacob Zuma mai shekaru 72 da haifuwa na jam'iyyar ANC '' African National Congress'' ta marigayi Nelson Mandela, ana sa ran zai sake samun nasara a zaɓen a gaban yar takarar jam'iyyar adawa. Duk kuwa da irin sukar da gwamnatinsa ta ke sha daga al'ummar ƙasar da kuma 'yan adawa da ke yi masa zargin cin hanci da karɓar rashawa da kuma gazawa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu