An fara ganawa tsakanin Bush da al-maliki | Labarai | DW | 30.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara ganawa tsakanin Bush da al-maliki

An fara ganawa tsakanin shugaba Bush na Amurka da firaministan Iraqi Nuri al-maliki a kasar Jordan akan hanyoyin da zaa kawo karshen tashe tashen hankula a Iraqi.

A tun jiya laraba Bush yake sa ran ganawa da al Maliki da sarki Abdallah na Jordan,amma daga bisani aka sanarda shi cewa Jordan da Iraqi sun yanke shawarar cewa ba dole ne su gana dukkaninsu uku tare ba.

Tunda farko dai an shirya ganawarce ta kawanki 2 tsakanin Bush da Maliki a jiya tare da nufin karfafawa shugaban na Iraqi gwiwa don fuskantar kalubale dake gabansa na tsaro,siyasa da tattalin arzikin kasarsa.

Daga karshe dai sarki Abdallah ya gana da shugabanin a lokuta daban daban a jiyan.

Kakakin fadar white House yayi watsi da batun cewa wannan canji na nunin cewa al-Maliki ya gwale shugaba Bush ne.