An fara bincike kan Mursi
July 13, 2013Talla
Ofishin babban mai bincike na gwamnatin Masar din ne ya tabbatar da wannan labarin a wannan Asabar din (13. 07. 13), inda ya ce daga cikin abubuwan da su ke binciken sun hada da korafi na leken asiri da kitsa kisan masu zanga-zangar lumana da tabarbarewar tattalin arzikin kasar lokacin da ya ke kan mulki.
To sai dai yayin da aka fara gudanar da wannan bincike, Amirka da tarayyar Jamus a wannan Juma'a (12. 07. 13) sun yi kiran da a saki Mursin daga inda soji ke tsare da shi tun bayan da suka yi masa juyin mulki.
Su kuwa magoya bayan Mursi din na ci gaba da yin zanga-zanga ce domin neman a saki hambararren shugaban da ma dai maida shi kan karagar mulki.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh