Interpol ta shiga cikin binciken FIFA
June 3, 2015A dangane da badakalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol ta sanya sunayen tsoffin jami'an FIFA a jerin wadanda ake gudanar da bikcke kansu. Amirka ce ta gabatar da bukatar sanya sunayen mutanen su shida da suka hada da Jack Warner daga Trinidad and Tobago, da Nicolas Leoz daga Paraguay, da kuma wasu shugabannin kamfanoni hudu daga kudancin Amirka. Ana zarginsu da aikata manyan laifuka da cin hanci da rashawa. Binciken cin hancin da aka kaddamar a kasashen Amirka da Switzerland an mayar da hankali kan zargin cewa an raba na goro lokacin ba da cancantar karbar bakoncin gasar kwallon kafa. A dangane da badakalar cin hancin, a ranar Talata ba zato ba tsammani shugabanin FIFA Joseph Blatter ya ba da sanarwar yin murabus.