1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sake dawo takarar dan adawa

Suleiman Babayo USU
August 30, 2024

Kotun Tunisiya ta sake ba da umurnin mayar da sunan daya daga cikin fitattun 'yan siyasar kasar Imed Daimi dan takarar shugaban kasa a zaben da ke tafe, wanda tun frako hukmar zabe ta yi watsi da takardunsa.

https://p.dw.com/p/4k7DA
Shirye-shiryen zaben Tunisiya
Shirye-shiryen zaben TunisiyaHoto: Yassine Gaidi/AA/picture alliance

Kotun kula da harkokin mulki ta kasar Tunisiya ta amince da bukatar daya daga cikin fitattun 'yan siyasar kasar Imed Daimi na saka sunansa a jerin 'yan takara a zaben shugaban kasar da aka tsara ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa.

Yanzu haka Imed Daimi ya zama mutum na uku da kotu a kasar ta ba da umurnin a mayar da sunansa daga cikin wadanda aka yi watsi da takardunsu na takara a zaben da ke tafe, inda tun farko aka mayar da sunayen Abdellatif Mekki da Mondher Znaidi.

Ana zargin hukumar zaben kasar ta Tunisiya da ke yankin arewacin Afirka da nuna rashin sanin makamar aiki gami da zama karen farautar bangaren zartaswa. Shi kansa Shugaba Kais Saied yana cikin yan takara wanda yake neman wa'adi na biyu na mulki, duk da zargin da ake masa na zama dan kama karya.