An daure tsohon minista a Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 27.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daure tsohon minista a Cote d'Ivoire

An daure tsohon minista Hubert Oulaye na gwamnatin Cote d'Ivoire na tsawon shekaru 20 saboda hannu a wani hari da ya hallaka mutane 18.

An daure wani tsohon minista a gwamnatin Cote d'Ivoire na tsawon shekaru 20 a gidan kurkuku saboda hannu kan wani hari da aka kai a yankin yammacin kasar a shekara ta 2012, abin da ya janyo mutuwar mutane 18 ciki har da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Hubert Oulaye dan shekaru 64 da haihuwa ya kasance ministan kula da ayyukan karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Laurent Gbagbo, kuma ana zargi ya kafa kungiyar tsageru masu dauke da makamai bayan da Gbagbo ya sha kasa a zabe, kuma an kai harin lokacin da kasar take murmurewa daga rikicin da ya biyo bayan zaben, bayan Shugaba Alassane Ouattara ya dauki madafun ikon kasra ta Cote d'Ivoire.

Sai dai Oulaye ya musanta tuhumar da aka yi masa a matsayin bita da kullin siyasa, sannan ya sha alwashin daukaka kara.