An daure tsohon jami′n MDD kan cin zarafi | Labarai | DW | 09.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daure tsohon jami'n MDD kan cin zarafi

Wata kotu a kasar Nepal ta yanke hukuncin dauri a gidan yari ga wani tsohon jami'in majalisar dinkin duniya da aka samu da laifin lalata da kananan yara.

Kotun ta ce Peter John Dalglish mai shekaru 62 dan kasar Kanada zai shafe shekaru 15 bisa laifin cin zarafi da lalata da kananan yara, tare da biyan diyyar dala 4,550 ga yaranda ya ci zarafinsu.

Sai dai tsohon jami'an na MDD ya musanta laifukan da kotun ke tuhumarsa da aikatawa, kuma lauyoyin da ke kareshi a kotu sun ki cewa komai kan hukuncin shari'ar.