An daure masu yaki da bauta a Moritaniya | Labarai | DW | 30.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daure masu yaki da bauta a Moritaniya

Shekaru goma masu yaki da ayyukan bauta goma za su shafe a gidan yari sakamakon gangamin yin tir da wannan dabi'a da suka gudanar a wasu sassa na kasar Moritaniya.

Wata kotu a birnin Rosso dake kudancin Mauritaniya ta yanke wa masu yaki da ayyukan bauta su goma hukuncin shekaru goma a gidan yari, sakamakon samunsu da ta yi da shiga cikin kungiyoyin da ba a amince da su ba.

Tun a watan nowmba ne dai aka cafkesu a lokacin da suke gudanar da kamfein yin tir da ayyukan bauta dake ci gaba da gudana a kasar. Majalisar tarayyar Turai ta albarkanci wani kudiri a kwanakin baya dake neman a sako masu yaki da ayyukan bautar ba tare da bata lokaci ba, lamarin da shugaban ya yi watsi da shi.

Shi ma lauyansu Lo Guirmo Abdel ya danganta hukunci da bita da kullin siyasa. Ya ce "Akwai wata manufa da kotu ma'ana gwamnati ta sa a gaba na sanya siyasa a harkokin da suka shafi shari'a. Ba ta dogara a kan abubuwa na zahiri ba wajen yanke wannan hukuncin. Amma kuma ta riga ta tanadi hukunci tun ma kafin a yi zaman kotun"

Ana ci gaba da gudanar da ayyukan bauta a Moritaniya duk kuma da cewar kasar ta haramta wannan dabi'ar tun shekaru 33 da suka gabata.