1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakile yunkurin juyin mulki a Kwango

May 19, 2024

Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango ta ce ta dakile wani yunkurin juyin mulki a kusa da offishin shugaban kasa, Felix Tshisekedi da ke birnin Kinshasa.

https://p.dw.com/p/4g3Hr
Videostill | Felix Tshisekedi im DW Interview
Hoto: DW

Rundunar ta ce an yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a kofar gidan ministan kula da tattalin arziki da ke yankin Gombe, inda nan ne offishoshin shugaban kasar suke. Kawo yanzu dai kakakin rundunar sojin, Sylvain Ekenge bai yi wani karin bayani ba dangane da yunkurin hambarar da gwamnatin. 

Karin bayani: AU ta yi tir da juyin mulki a Afirka

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya, Jakadan kasar Japan a Kinshasa, Kidetoshi Ogawa ya ce ministan bai samu rauni ba a harin da aka kai, sai dai an kashe jami'an 'yan sanda biyu da kuma mahari daya. An kuma ruwaito cewa, kura ta lafa a halin yanzu.

Tuni dai Jakadun kasashen ketare a kasar suka fara bukatar 'yan kasarsu da kaurace wa yankin da lamarin ya faru.