An dakile wutar gobarar da ta tashi a Dubai | Labarai | DW | 01.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakile wutar gobarar da ta tashi a Dubai

Rahotanni daga Dubai na cewar jami'an kwan-kwana sun yi nasarar dakile wutar gobarar da ta tashi a babban Otel na The Adress Downtown wanda ke a hawa na 63 na wani dogon bene na tsakiyar birnin na Dubai.

Rahotanni daga Dubai na cewa jami'an kwan-kwana sun yi nasarar dakile wutar gobarar da ta tashi a babban Otel na The Adress Downtown wanda da ke a hawa na 63 na wani dogon benen na tsakiyar birnin na Dubai.Sai dai har kawo yanzu hayaki na ci gaba da tashi a cikin ginin wanda ya kama da wuta da misalin karfe tara da rabi na daren jiya Alhamis. Hukumomin birnin dai sun ce mutane 14 suka ji rauni akasari dan kankane a cikin gobarar.

Sai dai wata majiyar wani gidan assibiti inda aka dunga kai mutanen da gobara ta shafa ta ce mutane kimanin 60 aka yiwa binciken lafiya akasarinsu sakamakon shakuwa da hayaki mai guba a lokacin gobarar.Sai dai wannan gobara ba ta sa hukumomin birnin sun soke bukukuwan dama wasan wuta da aka tsara za a yi albarkacin shiga sabuwar shekara ta 2016 ,kuma tuni aka soma gudanar da bincike na gano musabbabin tashin wannan gobara