An dakatar da wasu alƙalai a Ghana | Labarai | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakatar da wasu alƙalai a Ghana

Hukumomin shari'a a Ghana sun dakatar da aikin wasu alƙalai guda 22 saboda zargin cin hanci.

Ghana Präsident John Dramani Mahama

Shugaban Ghana John Dramani Mahama

Wannan lamari ya biyo bayan da wani ɗan jarida mai yi aikin bincike,ya fitar da wani faifan bidiyio wanda ke nuna ƙarara alƙalan sun amince suka karɓi cin hanci.Ɗan jaridar mai sunan Anas Aremeyaw Anas ya miƙa hotunan bidiyion ga mahukunta shari'a na ƙasar wanda a ciki alƙalai da dama ke da hanu a cikin lamarin na karɓar na goro.

A shekarun 2014 a rahoton da ƙugiyar yaƙi da cin hacin ta Tranparency Interational ta bayyana, Ghana ita ce ta 61 cikin ƙasashe 175 a duniya a kan batu na yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa.