1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin matuka jiragen sama ya haifar da tsaiko a Sufuri

Zulaiha Abubakar
September 9, 2019

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya dakatar da wasu daga cikin jiragen kamfanin masu jigila a Birtaniya, kwana guda bayan da matukan jiragen suka tsunduma yajin aiki.

https://p.dw.com/p/3PGNp
London Heathrow Airport British Airways Flugzeug
Hoto: Reuters/H. McKay

A wata sanarwa da kamfin ya fitar, ya bayyana gazawa wajen a warware batun karin albashi tsakaninsa da kungiyar matuka jirage a matsayin daliin dakatar da sufurin jiragen da kamfanin ya yi a wannan Litinin din. Kungiyar matukan jiragen ta kwashe watanni tara tana bukari gyaran albashi da ingancin yanayin aiki. Dubban matafiya sun fuskanci tsaiko a tafiye-tafiyensu sakamakon wannan dakatarwa.