An dakatar da Afirka ta Tsakiya daga AU | Siyasa | DW | 25.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An dakatar da Afirka ta Tsakiya daga AU

A martaninta na farko biyo bayan juyin mulkin da 'yan tawaye suka yi a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kungiyar tarayyar Afirka ta dakatar da kasar daga zama mamba a cikinta.

Shugaban Kungiyar 'yan tawayen Seleka da suka yi Juyin mulki a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya Michel Djotodia, ya sha alwashin nada kansa a mukamin shugaban kasar tare kuma da kafa gwamnatin hadin gwiwa. Wannan dai ya zo ne a dai dai lokacin da Kungiyar tarayyar Afirka wato AU ke bayyana dakatar da kasar daga zama mamba a kungiyar.

Sabon shugaban karkashin kungiyar 'yan tawayen ta Seleka Michel Djotodia mai kimanin shekaru 60 da haihuwa wanda kuma tsohon ma'aikacin gwamnati ne, ya kwashe shekaru da dama a Tarayyar Sobiet, ya bayyana cewa nan da shekaru uku masu zuwa za su tabbatar da ganin an gudanar da zabe mai inganci domin kafa gwamnatin demokradiyya a kasar, kuma ya shaida wa manema labarai cewa ba wai ya ce zai sauka daga kan karagar mulki nan da shekaru uku masu zuwa ba ne, sai dai ya ce zai shirya sahihin zabe cikin shekaru uku masu zuwa.

Al'umma dai na ci gaba da bayyana ra'ayinsu kan wannan juyin mulki kamar yadda wani dan jarida a kasar Patrice Zemoniako ke cewa akwai abubuwan da ya kamata 'yan tawayen su yi kafin karbe mulkin.

"Mutane na ta yin wasoso, kuma ya fi yawa a birnin Bangui, abin da ya kamata 'yan kungiyar Seleka su yi kafin su iso Bangui, shi ne na daukar matakan tsaro domin kiyaye kamfanoni da masana'antu, to ba su yi haka ba, yanzu duk an sace wa jama'a kayan sana'arsu, wannan abu ne da zai haifar da ɓacin ran al'umma."

Ba za a yi bita da kulli ba

Tsohon ministan noma da raya kasa a lokacin gwamnatin Francoise Bozize, Fidele Ngoundjika ya baiyana cewar sabon shugaban kasar ya tabbatar musu da cewar ba zai dauki wani mataki kan tsofaffin jami'an gwmanati ba a ganawar da suka yi da shi.

"Na samu na gana da shi kuma ya tabbatar mani da cewar ba za su yi bita da ƙuli ba ga tsofin jami'an gwamnati ba, ya ce kuma a shirye ya ke ya yi aiki tare da kowa, a kan haka mu ma a shirye mu ke mu yi aiki saboda ci gaban kasar mu ba tare da nuna son kai ba."

Matakin AU a kan masu juyin mulki

Kungiyar tarayyar Afirka, AU ta bayyana cewa ta dakatar da jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya daga kasancewa mamba a cikinta har sai sun koma kan tsarin mulki tare kuma da sanya takunkumi ga kungiyar 'yan tawayen da suka yi wa shugaba Francoise Bozize juyin mulki.

Kungiyar tace takunkumin ya hadar da hana 'yan kungiyar tawayen ta Seleka yin tafiye tafiye da taba kadarorinsu tare kuma da umartar dukkan gwamnatocin kasashen Afirka da su yi watsi da gwamnatin da ba halastacciya ba, tare da yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Turai da suma su yi watsi da gwamnatin da tsarin mulki bai amince da ita ba.

An dawo daga rakiyar Bozize

Wani jami'i a cibiyar Chatham dake London Paul Melley, yace yana ganin al'ummomin duniya sun dawo daga rakiyar shugaba Bozize ne saboda gwamnatinsa ta gaza aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma watanni biyun da suka gabata ba, shi ne ya sanya ba su dauki wani kwakkwaran mataki na dakile yunkurin 'yan tawayen ba kuma kungiyar na son tirsasa 'yan tawayen su koma kan turbar demokradiyya.

"Ina ganin kungiyar tarayyar Afirka na so ta tursasa 'yan tawayen Seleka su gaggauta daukar matakan komawa kan kundin tsarin mulkin kasar."

Kasar Chadi dai na daya daga cikin kasashen da suka mara wa Bozize baya yayin juyin mulkin da ya bashi damar darewa kan karagar mulki a shekara ta 2003, sai dai a wannan lokacin ba ta bada gudunmawar sojoji domin kare kasar ba, wanda hakan ya sanya ake ganin kamar ita ma ta dawo ne daga rakiyarsa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapah Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin