An dage cigaban shariar Sadam zuwa 24 ga Afrilu | Labarai | DW | 19.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage cigaban shariar Sadam zuwa 24 ga Afrilu

Irak

An sake dage sauraron shariar tsohon shugaban Iraki Sadam hussein ,zuwa ranar 24 ga wamman wata da muke ciki.Mai shari Rauf Abdel Rahman yace an dage shariar ne,domin bada karin lokaci wa masu shigar da kara na tabbatar rattaba hannun daya daga cikin wadanda ake karanMizhar Abdallah Ruweid,dake kann wata takardar dake danganta shi da kisan kiyashi da akayi a kauyukan Dujail a t shekara ta 1982.A yayin sharia tayau dai Alkalin kotun ya hakikance cewa Rattaba hannun Sadam ne akan wasu takardu dake bada umurnin kashe shiyawa 150,wanda kuma idan aka tabbatar da laifin akansa ,zai fuskanci hukuncin kisa.