An daga lokacin zaben shugaban kasar Kwango | Labarai | DW | 16.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An daga lokacin zaben shugaban kasar Kwango

Hadin gwiwar jam'iyyun da ke mulki a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da kuma wani bangare na 'yan adawa sun cimma matsaya ta dage lokacin zabe ya zuwa watan Afirilu na 2018.

Cikin wata sanarwa ce dai da ta fitar, jam'iyyar UNC da ke a matsayin babbar jam'iyyar adawa a kasar ta Kwango da ta kasance cikin tattaunawar, ta tabbatar da samun daidaito wajen tsayar da wannan sabon wa'adin zaben shugaban kasar, inda ta ce an kuma rarraba mukamai tsakanin bangarorin amma kuma shugaba Kabila zai ci gaba da zama shugaban kasa.

Sanarwar ta jam'iyyar UNC ta ce tattaunawar ta amince da bada mukamin Firaminista ga wakilin 'yan adawa wanda kuma ake ganin ba kowa ba ne illa shugaban jam'iyyar ta UNC Vital Kamerhe. Sai dai mafi yawan jam'iyyu na bangaran adawa sun ki halartar wannan zama inda suka ce wata makarkashiya ce don kawai Shugaba Kabila ya ci gaba da zama kan karagar mulkin kasar.

Tuni dai 'yan adawan kasar ta Kwango suka kira yajin aiki na gama gari daga ranar Laraba mai zuwa a wani mataki na nuna kin amincewarsu da duk wani tsari na tsayawar Shugaba Kabila bayan wa'adin mulkinsa da ke karewa a ranar 19 ga watan Disamba.