An cimma yarjejeniyar kafa kwaryakwaryar gwamnati a Birtaniya | Labarai | DW | 26.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma yarjejeniyar kafa kwaryakwaryar gwamnati a Birtaniya

Jam'iyyar Conservative a Birtaniya ta cimma yarjejeniya da DUP ta Ireland ta Arewa kan gwamnati maras rinjaye.

Großbritannien Theresa May mit Arlene Fostervor 10 Downing Street (Reuters/S. Wermuth)

Theresa May ta jam'iyyar Conservative da Arlene Foster ta jam'iyyar DUP

Shugabar jam'iyyar Democratic Unionists Party wato DUP a lardin Ireland ta Arewa, Arlene Foster ta tabbatar cewa ta cimma yarjejeniya da jam'iyyar Conservative ta Firaministar Birtaniya Theresa May don mara baya ga gwamnatinta maras rinjaye.

Foster ta ce Firaminista May ta amince ta tallafa wa Ireland ta Arewa da dala miliyan 1.9 sai dai bata yi karin bayani. Ta nuna jin dadinta da cimma yarjejeniya da ta ce nan gaba kadan za a yi bayani dalla-dalla kan ka'idojinta.

Ta ce: "Bayan sakamakon babban zaben da aka gudanar da ikon da al'ummar Ireland ta Arewa ta bamu, Conservative da DUP sun yi ta tattaunawa kan yadda za mu mara wa gwamnatin tsiraru ta Conservative baya a majalisar dokoki. A yau mun cimma yarjejeniya bisa wannan manufa. Yarjejeniyar za ta yi aiki don samar da kwakkwarar gwamnati da za ta kare muradun Birtaniya a wannan lokaci mai muhimmanci."