An cimma sulhu a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango | Labarai | DW | 31.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cimma sulhu a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango

'Yan adawa da gwamnati a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango sun cimma sulhu bayan da aka kwashe makonni biyu ana tataunawa da nufin warare rikicin siyasar kasar.

 

Rikicin siyasar dai ya  samo asili ne bayan da shugaba Joseph Kabila ya ki sauka daga mulki a karshen wa'adinsa a ranar 20 ga wannan wata na Disamba da ke shirin kammala.Wani kakakin jami'an Cocin Roman Katolika na kasar da ke shiga tsakanin ya ce yau aka shirya za a baiyana sanarwa yarjejeniyar da za a  rataba hannu a kanta.Kuma daya daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta tanada shi ne cewar joseph kabila zai ci gaba da yin mulki har zuwa sabuwar shekara ta 2017,lokacin da a aka shirya yin wani sabon zabe a kasar, sannan za a nada sabon firaminista da ya fito daga bangaran 'yan adawa.