1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta sake duba batun 'yan cirani

Zulaiha Abubakar
July 3, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta amince da batun tsaron iyakokin kasar don magance kwararar 'yan cirani,lamarin da ya zama barazana ga cigaban dorewar gwamnatin hadakar kasar ta Jamus.

https://p.dw.com/p/30iI8
Auftakt Klausur CSU-Landesgruppe
Hoto: picture alliance/dpa/N.Armer

A jiya litinin ne dai Shugabannin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma jam'iyyar CSU wadda Horst Seehofer ke jagoranta suka gana a birnin Berlin don nemo bakin zaren rikicin dake shirin ballewa a fadar mulkin kasar, bayan da ministan cikin gida yayi barazanar sauka daga kujerar sa matukar Merkel din ba ta dauki matakin gaggawa kan bakin da suka kasar ta Jamus ba.