An ci tarar kamfanin Volkswagen a Amirka | Labarai | DW | 21.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ci tarar kamfanin Volkswagen a Amirka

Kotun Amirka ta tabbatar da wata yarjejeniyar da kamfanin Volkswagen ya cimma da hukumomin Amirkar da ta tanadi biyan tarar kudi ta kusan biliyan uku na dalar Amirka a kan badakalar injinan Diesel da aka yi almundahana.

Wata kotun kasar Amirka ta tabbatar da wata yarjejeniyar da kamfanin motoci na Volkswagen ya cimma da hukumomin Amirkar da ta tanadi biyan tarar kudin kisan laifi miliyan dubu biyu da dari takwas na Dalar Amirka a kan badakalar motoci masu injinan Diesel na jabu da kamfanin ya sayar a kasar ta Amirka. 

Alkalin kotun ya umurci kamfanin na Volkswagen wanda shi ne kamfanonin motoci mafi girma a duniya da ya biya wadannan kudin tara a cikin shekaru uku masu zuwa. A watan Satumbar shekara ra 2015, kamfanin na Volkswagen ya amince da sayar da motoci miliyan goma 11 masu dauke da injin Diesel na jabu da ke boye hakikanin yawan gurbataccen hayakin da injin motar ke fitarwa. 

A Jumulce dai kudi tsaba miliyan dubu 23 na dalar Amirka ne kamfanin na Volkswagen zai zuba wa kasar ta Amirka domin kisan laifi ga mutane dubu 600 da kamfanin ya sayar wa da motocin masu injinan na jabu.