An ceto ma′aikatan ma′adanai a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 02.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto ma'aikatan ma'adanai a Afirka ta Kudu

Aikin ceton ya fuskanci kalubale kasancewar ma'aikatan ma'adanan sun makale a rami mai zurfin mita 700 zuwa mita 2000 a karkashin kasa.

Ma'aikatan ceto a Afirka ta Kudu sun sami nasarar ceto dukkan ma'aikatan hakar ma'adai su 955 wadanda suka makale a karkashin kasa sakamakon katsewar wutar lantarki a mahakar zinare ta Beatrix dake kasar.

Hukumomi sun ce an ceto dukkan mutanen a ranarJuma'ar nan kuma babu wanda ya sami ko da kwarzane.

Dangi da 'yan uwan ma'aikatan sun yi ta sowa da murna yayin da aka fito da su daga karkashin kasar.

Kungiyar ma'aikatan ma'adanan ta yi kiran yayanta su bujire wa aiki a wurare masu hadari domin kare lafiyarsu.

Kwamitin majalisar dokokin Afirka ta Kudu mai kula da aikin hakar ma'adanai ya baiyana damuwa da aukuwar lamarin inda ya bukaci kamfanin ya dauki matakai domin kare aukuwar irin hakan a gaba.