An ceto daruruwan bakin haure a tekun Bahar Rum | Labarai | DW | 15.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto daruruwan bakin haure a tekun Bahar Rum

'Yan gudun hijira fiye da dubu biyu masu gadin gabar tekun Italiya suka ceto daga tekun Bahar Rum a cikin kwanakin nan.

Wasu bakin haure kimanin 480 sun isa tashar ruwan garin Palermo na kasar Italiya a cikin jiragen ruwa guda uku. Mutanen da rahotanni suka ce 'yan asalin kasar Somaliya ne a ranar Talata dakarun tsaron iyakokin ruwan kasar Italiya suka ceto su a kusa da gabar tekun tsibirin Sicily. Da sanyin safiyar wannan Larabar kuma wasu bakin haure fiye da dubu daya da dari daya sun isa a yankin, sannan masu gadin iyakokin ruwan Italiya sun ce a ranar Talata kadai sun ceto karin bakin haure 1500 daga wasu jiragen ruwa marasa inganci. Yawan mutanen da aka ceto a cikin kwanakin nan sun kai dubu 10. Hakan dai na zuwa ne bayan da a ranar Talata wasu bakin haure 400 suka rasu lokacin da suke kokarin kai wa Italiya daga Libya, bayan da jirgin ruwansu ya nitse a tekun Bahar Rum.