1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Malesiya sun tsere tsohon firaminista

September 19, 2018

Hukumomin Malesiya sun tsere tsohon Firaminista Najib Razak bisa tuhumar cin hanci da rashawa lokacin da yake rike da madafun iko kasar.

https://p.dw.com/p/35AfV
Malaysia Kuala Lumpur Najib Razak vor Gericht
Hoto: Getty Images/AFP/M. Rasfan

Hukumomin kasar Malesiya sun cafke tsohon Firaminista Najib Razak bisa tuhumar almundahana da makuden kudade lokacin da yake rike da madafun iko. Akwai miliyoyin kudade da aka samu a asusun ajiya na tsohon firamnistan, maimakon zuba jari kamar yadda aka tsara na gwamnati.

Tun lokacin da Najib Razak ya sha kaye a zaben kasar ta Malesiya na watan Mayu, sabon firaminista da aka zaba Mahathir Mohamad dan shekaru 92 ya bude bincike game da zargin cin hanci ga gwamnatin da ta gabata. Hukumar yaki da cin hanci ta kasar ta Malesiya ta ce tana tsare da tsohon Firaminista Najib bisa tambayoyin kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.